4 Maris 2018 - 15:42
MDD ta dakatar da ayyukan agaji a Rann

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan agaji ga dubban ‘yan gudun hijirar da ke sansanin garin Rann a jihar Borno da ke Najeriya, a dalilin harin da mayakan Boko Haram suka kai kan barikin soji inda suka hallaka wasu jami’an agaji 3, wasu 3 kuma suka bace.

Sanarwar ta Majalisar dinkin duniya a Juma’ar da ta gabata, ta bayyana janye jami’anta baki daya guda 40 da ke ayyukan agaji a sansanin na Rann mai dauke da ‘yan gudun hijira akalla dubu 55,000.

Zalika an dakatar da kai kayayyakin agaji zuwa sansanin ‘yan gudun hijirar.

A daren ranar Juma’a itama kungiyar Likitoci ta kasa da kasa Medecins sans Frontieres ta sanar janye ayyukanta a sansanin na Rann, sakamakon harin na mayakan Boko Haram.